Daga farkon shekarar 2022 zuwa yanzu kusan ƙarshen 2023, wani rahoto ya bayyana cewar kimanin Magidanta 7, da Matan aure 21, gami da ‘yan mata 6 ne suka rasa ransu a wani yanayi mai alaƙa da rikicin zamantakewa.
Rahoton wanda jaridar Daily Trust ta tattaro tare da wallafawa, ya bayyana yanda wasu dalilai ke zama sanadin samun saɓani da har a ƙarshe ake asarar rayukan.
Wanda bisa bayanai da aka tattaro, ya nuna yanda kowanne sashe na ƙasa ke fama da matsalar.
Babban dalilin da rahoton ya wallafa shine matsalar kuɗi. Kuɗi ya na da tasiri sosai a zaman lafiyar aure, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa. Shi yasa idan ma’aurata suka wayi gari a cikin ƙaranci ko ma rashin kuɗin baki ɗaya, sai matsaloli su fara tasowa da za su haifar da saɓani.
Abu na biyu akwai cin amana. Rahoton ya haska yanda ɓangarori biyu na ma’aurata ke cin amanar juna, wanda daga ƙarshe asiri yake tonuwa har kuma ta kai ga mummunan rikicin da zai iya sanadin abokan zamansu.
Abu na ƙarshe akwai rashin fahimtar juna, ko uzuri ga abokan zaman ga ma’aurata. Ba shakka hakan na taka rawa wajen saurin kawo saɓani ga ma’aurata.
Daga ƙarshe rahoton ya bayar da shawarwari don ganin an gujewa faɗawa tarkon nadama a dalilin rikicin auren.
Leave a Reply