Tsananin takaici ya sa wani manomi bindige makiyayi har lahira

0
237

An shiga ruɗani a yankin Ago-Owu na ƙaramar Ayedaade da ke jihar Osun, bayan da aka tsinci gawar wani Makiyayi a wata gona.

A cewar rahotanni, mai gonar mai suna Paul Amaechi ya jima yana sanar da ‘yan uwansa ta’adin da dabbobi suke masa a gona.

Sai dai ta’adin da aka yi masa a ranar 10 ga watan Nuwambar shekarar 2023 shi ya fi ɗaga masa rai. Wannan lamari ne ya sa ya kuma ɗaukar ɗamarar ɗaukar matakan kare gonarsa.

Kimanin sati biyu da yin wancan ta’adi, Makiyayin tare da abokin kiwonsa, suka kuma mamaye gonar Paul. Daganan ne ya taso musu, nan take hayaniya ta kaure, lamarin da ya yi sanadin Paul zaro bindiga tare da harbe Bafulatanin nan take.

Abokin kiwonsa da ya arce, shine ya sanar da Arɗonsu halin da ake ciki. Daganan aka sanar da hukumar NSCDC, suka ke suka ɗauko gawar mamacin.

A lokacin da suke binciken gidan Paul, jami’yan tsaron sun samu bindigar da ya yi harbin da ita, tare da wasu makamai a tare da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here