
Wani bawan Allah wanda ya kasance cikin wata rayuwa mai abin mamaki, ya kuma jefa al’ummar garin Haɗejia cikin wani mamakin, a sa’ilin da wata tawagar mutane suka dira garin don saduwa da mutumin.
A cewar wani mazaunin garin na Haɗejia, Aji Kima, kamar yanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, mutumin mai suna Malam Ya’u ya shafe shekaru sama da arba’in ya na rayuwa a garin Haɗejia, kuma ba wata sana’a da ya ke yi sai faskare. Idan kuma dare ya yi, sai ya tafi maƙabartar Makara-Huta ya yi kwanciyarsa har zuwa wayewar gari ba tare da wata matsala ba.
Malam Ya’u, wanda mutane da dama suke yi a laƙabi da “Innabalaun” ya yi sabo mai yawa da mutanen da ke unguwannin Majema, Sabon garu, Gagulmari, Matsaro, Gawuna, Shagari da su Jama’are.
Zuwan ‘yan uwansa ne aka fahimci cewar ashe ɗan asalin Bauchi ne. Kuma tuni aka shirya shi tsaf don komawa gida wajen ‘yan uwansa, bayan shafe wannan lokaci da Haɗejawa.
