Kano Times

Nothing but authentic

Marubuta a Kano sun buƙaci da a yiwa waɗanda sojoji su ka yiwa luguden bam Adalci

Marubuta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun yi kira da a yi wa waɗanda su ka iyalan wadanda su ka rasa rayukansu a harin da aka kai da jiragen yaƙi marasa matuka a yayin wani taron mauludi a unguwar Tudun Biri, jihar Kaduna Adalci.

Marubuta sun bayyana ne haka a wata zanga-zangar lumana da su ka gudanar kamar yadda mataimakiya ta musamman ga gwamnan Kano akan harkokin jin ƙai Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Talata.

Haka kuma marubuta na dauke da kwalaye da aka yi rubuta daban – daban da su ke nuni da a yiwa wadanda harin ya shafa Adalci.

Al’ummar Najeriya da dama sun nuna fusata kan lamarin, wanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kai.

Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasa ta bayyana cewa mutum 85 ne suka rasu sanadiyyar harin, yayin da wasu mutanen 60 suka samu rauni, sai dai ƙungiyoyin masu kare hakkin bil’adama na ganin cewa alƙaluman sun zarce haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *