Yadda wasiƙar Sheikh Dahiru Bauchi ta haifar da ruɗani game da shari’ar zaɓen gwamnan Kano

0
630

Ga alamu akwai ruɗani da kuma rabuwar kai game da sahihancin wasiƙar da aka ce jagoran ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya rubuta yana neman Kotun Ƙolin Najeriya ta yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano.

A ranar Juma’a ne wasiƙar mai ɗauke da sa hannun shehin malamin ta karaɗe shafukan intanet da kwanan watan 1 ga watan Disamban 2023, wadda kuma aka rubuta wa Babban Alƙalin Najeriya Olukayode Ariwoola.

A ranar Asabar ɗaya daga cikin ‘ya’yan malamin mai suna Naziru Dahiru ya tabbatar wa da BBC Hausa cewa da gaske mahaifinsa ne ya rubuta wasiƙar.

Sai da kuma, jim kaɗan bayan wasu kafofin yaɗa labarai sun wallafa labarin, Sheikh Bashir Dahiru – wani daga cikin ‘ya’yan malamin – ya faɗa wa BBC Hausa cewa takardar ba ta gaskiya ba ce.

“Yadda kuka ga takardar nan haka muka gan ta, shehi ya ce ba shi ne ya rubuta ta ba, bai san da ita ba,” kamar yadda ya bayyana a hirar da aka yaɗa a labaran BBC na safiyar yau Lahadi.

Har wa yau, an ji wani saƙon murya ta Sheikh Dahiru Bauchi da kansa yana musanta rubuta wasiƙar, yana mai cewa bai san da ita ba kuma ba daga wajensa ta fita ba.

A gefe guda kuma, Naziru Dahiru Bauchi ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook – mai suna Naziru Tahir – ranar Lahadi yana jaddada iƙirarin cewa shi ne ya kai wa kotun ƙoli wasiƙar da hannunsa bayan mahaifin nasa ya amince da ita.

“Ni ne wanda shehi ya aika na kai wasiƙa wajen babban alƙali wadda take yawo a soshiyal midiya [shafukan sada zumunta], kuma na kai, sun ba ni takardar cewa sun karɓa,” a cewarsa.

Sai dai ya tabbatar da cewa shi ne da kansa ya je ya nemi mahaifin nasa ya saka baki a batun shari’ar don ya yi kira da a yi adalci.

“Manyan ƙasa suna ta saka baki, suna kiran a yi adalci, shi ne muke neman izininku ku ma ku ja hankali lallai cewa ba a son abin da zai taɓa Kano, idan wani abu ya taɓa Kano zai taɓa ƙasa duka,” kamar yadda aka ji Nazirun yana faɗa wa mahaifin nasa ta waya a cikin bidiyon da ya wallafa.

Sai dai ba a ji amsar da mahaifin nasa ya ba shi ba kafin ya katse sautin, kuma kalaman nasa sun yi kama da waɗanda wasiƙar ta ƙunsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here