EFCC Ba Ta Kai Sumame Kan Ofishin Mu Ba – Dangote

0
196

……Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC sun zo Babban Ofishin mu…

1.Kamar yanda akayi ta yada rahotannin zuwan Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa ta EFCC ta yi zuwa babban ofishin mu dake Jihar Lagos a ranar 4 ga watan Janairun 2024, mun fahimci irin karsashin da abokan huldar mu da kuma sauran al’umma suke dashi domin sanin hakikanin abinda ya faru.

A saboda haka mu ka ga muhimmancin sanar da ku hakikanin abinda ya faru a wannan rana.

2.A ranar 6 ga watan Disamba,2023 mun samu wasika daga Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa ta kasa wato EFCC, inda suke bukatar mu basu ba’asin Kudaden waje wato Dalar Amurka da Babban Bankin Najeriya ya bamu daga shekara 2014 zuwa yanzu.

Abin da ya kamata a fahimta shi ne ba kamfanin Dangote kadai aka baiwa wannan wasikar ba, an turawa wasu kamfanonin kimanin 51 irin wannan wasikar kuma suma ana neman wannan bayanin daga gare su.

3.Mun baiwa Hukumar EFCC takardar karbar bukatar da suka turo mana, muka kuma bukaci su yi mana Karin bayani a bangaren da suke bubatar bayanin, ko kuma daga wane bangare na rukunin kamfanonin mu.

Mun kuma bukaci karin lokaci domin hadawa tare da gabatar musu takardun da suka kai shekaru goma.

4.Haka Kuma, hukumar EFCC basu fayyace mana bangaren da suke da bukatar bayanan ba, kuma basu bamu damar da muka bukata daga gare su ba dangane da karin lokaci, suka kafe akan lallai suna da bukatar wannan bayanai a kurarren lokaci.

Duk da wannan ‘sa toka sa katsin’ da akayi, mun tabbatarwa hukumar EFCC cewa zamu gabatar musu da bayanan da suka bukata a lokuta daban da ban saboda muna kan kamala tattara bayanan.

  1. A ranar 4 ga watan janairu 2024, ma’aikatan mu suka fara mikawa Hukumar EFCC rahoto kashi na farko.

Baya ga haka, Jami’an hukumar EFCC suka ki karbar takardun rahoton da muka gabatar musu, suka ki amincewa da kai musu da akayi, suka ce sai dai suzo ofishin mu su karbi wannan kwafin rahoton da muka gabatar musu da kansu.

6.Duk da kasancewar ma’aikatan mu suna ofishin su da takardun bayanan da suka bukata, wasu daga cikin jami’ansu suka wuce zuwa ofisoshin domin karbar wannan rahoton da aka gabatar musu wanda hakan ya zubar mana da kima da kuma taba darajar mu.
Duk da yake jami’an nasu basu dauki wasu takardu ko kuma wani kundi daga ofishin namu ba a lokacin zuwan nasu, domin duk abinda suke nema yana ofishin su.

7.Muna fada da babbar murya cewa, babu wani zargi ko kuma wata badakala da ake zargin daya daga cikin rukunin kamfaninnikan mu da ita a wannan lokacin, face dai muna bayar da bayanan da aka bukata daga gare mu domin taimakawa hukumar EFCC a binciken da take yi.

8.A matsayinmu na kamfanin da yake biyaiya ga dokokin kasa, a shirye muke da mu bada hadin kai wajen baiwa hukumar EFCC duk wani bayani da suke da bukata daga wajen mu. Mun riga mun mika musu kason farko na bayanan da suka bukata daga gare mu, Mu na kuma aiki tukuru domin ganin mun basu sauran bayanan da suka rage daga gare mu akan lokaci, domin taimakawa binciken da suke yi.

  1. Gamaiyar Kamfanonin mu suna daga cikin wadanda suka fi bada gudunmawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar nan, kuma daya cikin manyan kamfanonin dake kasuwar hanneyen jarin kasar nan, sannan kuma daya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi biyan haraji mai yawa.

Mun kasance masu biyaiya ga dokin kasa tare da kare martabar ta a yunkurin da gwamnatin taraiya take yi na ganin an samar da bunkasar tattalin arziki ta yanda masu zuba hannayen jari na gida dana waje zasu sami damar yin hakan.

10.Muna kira ga abokan huldarmu su fahimci yanda abin yake, su kuma kwantar da hankalin su. Zamu ci gaba da sanar dasu duk halin da ake ci lokaci zuwa lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here