Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya, FRSC ta sanar da aukuwar wani mummunan haɗari a kan hanyar Kano zuwa Zaria a dai-dai mahaɗar Taban Sani, a Tashar Yari da ke kan babbar hanyar a ranar Lahadi 21 ga watan Janairun 2024.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun Kabir Y. Nadabo, wanda shi ne kwamandan shiyya na hukumar na cewa, haɗarin ya auku ne yayin da wata mota ƙirar Toyota Bus mai lamba TRB 674ZG 35XB ta taso daga jihar Kano zuwa Makurdi.
Mota kirar Toyota Bus mai lamba TRB 674ZG 35XB ta taso daga jihar Kano zuwa Makurdi
Da alama haɗarin direban motar ne shi kaɗai ya haddasa shi, a sakamakon gudun wuce gona da iri, inda direban ya rasa yadda zai sarrafa motar kuma ya kutsa cikin wani rami da ita.
Wata motar hukumar da ke sintiri a yankin ta sami sakon gagawa, inda ta isa wurin kuma jami’an hukumar suka gudanar da ayyukan ceto nan take.
“Binciken farko na hadarin ya tabbatar da mutum 20 ke cikin motar, 4 sun samu raunuka, kuma abin bakin ciki mutane 16 ne suka rasa rayukansu,” inji sanarwar.
An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin garin Maƙarfi domin yi musu magani cikin gaggawa, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zaria.
Shugaban shiyyar da wannan haɗarin ya auku ya kuma sanar da manema labarai cewa an tafi da jadawalin sunayen waɗanda haɗarin ya rutsa da su domin ƴan uwansu da abokai su taimaka wajen gano waɗanda suka kasance ba su, da waɗanda suke cikin mawuyacin hali a asibiti.