Sakin Murja Kunya daga gidan yari ya tayar da ƙura a shafukan sadarwa

0
368

Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da sakin da aka yiwa shahararriyar ƴar TikTok din nan yar jihar Kano Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali da tarbiyya.

Tun da farko Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama Murja Ibrahim Kunya ne da laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waɗanda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.

Haka kuma ana zargin Murja da yin amfani da kalaman ɓatanci da rashin kunya a cikin bidiyonta, wanda dubban mutane ke kallo

Kano Times ta tattaro ra’ayoyin jama’a a shafukan sada zumunta kan wannan batu.

Zulyadaini Sidi Mustapha wanda fitaccen ɗan jarida ne cewa ya yi “Malam Daurawa ka daina wahalar da kanka a aikin Hisba. Kai kadai ne kake yi da gaske amma shugabannin gwamnatinka makaryata ne mayaudara. Daga abinda akayi ga murja mun fahimci gwamnati bata da shaawar ganin an tsayar da shariar Allah a Kano. Hisba na hani da mummunan aiki Gwamnati na fada kyakyawan aiki. Ashsha.”

Shi kuwa Ahmad Lawan ga abin da ya ce ” GWAMNATIN ABBA ZATA BATA RAWARTA DA TSALLE.

SAKIN MURJA da akai, ta bayan fage, bayan Hizba sun gabatar da ita gaban alkali kuma alkali ya daureta, gatsali ne ga shari’ar Allah…

Kwanan muka dukufa ba ji ba gani muka koma gun Allah don yai mana maganin abinda duk duniya ba wanda muke dashi da zai mana, duk manyan kasa dana jaha suka juyawa gwamnati baya, yau Allah yaji rokon mu shine zamu fara kafirce masa, muna bawa masu yiwa dokokinsa karen tsaye kariya?

Anan dai kam wallahi GANDUJE yafi wannan gwamnatin.

Muyi a hankali, Allah nada hanyoyi kama bayinsa fiye da yadda muke tunani wallahi..

Allah kyauta.”

Yaushe gyara zai yiwu a haka. Muji tsoron gyaran Ubangiji matsawar muda kanmu muka kasa gyarawa.” In ji Bello Ahmad

“Maganar Murja me kunya fa Tana Neman zama abin kunya. Gidan yari sun ce alkali ya Aiko da takardar sakin ta,majiya daga kotu tace alkali bai bayar da belin ta ba,Shin Ina gizo ke saka?” In ji Nasiru Salisu Zango.

A makon jiya ne wata kotun shari’ar Musulunci ta aike da Murja gidan gyaran hali da tarbiyya sai dai kwana ɗaya a tsakani rahotanni su ka bayya cewa Ƴar TikTok din ta yi ɓatan dabo a gidan yarin.

Sai dai a yau Lahadi kakakin hukumar gayara hali da ke jihar Kano, Musbahu Lawal Kofar Nasarawa, ya sanar da manema labarai cewa an ba su umarnin sakin Murja Kunya ne a rubuce, kamar yadda aka ba su umarnin tsare ta tun da farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here