Kano: Hisbah Ta Yi Sammacin Mawallafin Jaridar Politics Digest, Adnan Tudun Wada

0
389

Hukumar Hisba a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta yi sammacin manajan kamfanin Dillancin Labarai da hulda da jama’a na PRNigeria, Adnan Mukhtar Tudun Wada da ke jihar akan wani labari da ya wallafa a jaridar Politics Digest.

A cikin labarin Adnan Mukhtar ya rawaito cewa fitacciyar ƴar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya ta yi zarge-zargen cin zarafi da jami’an hukumar ta Hisbah su ke yiwa mata idan sun kama su.

Tun da farko Dan jaridar ya samu kiran waya daga wani wanda ya gabatar da kan sa a ranar Alhamis, inda ya buƙaci ya gabata a gaban hukumar ranar Litinin.

Sai dai daga bisani Adnan din ya bukaci a turo da sakon gayyatar a rubuce a maimakon faɗa da Bala.

“Ana gayyatar ku zuwa Hukumar Hisba ranar Litinin bayan karfe 2 na rana don tattaunawa.”

Gayyatar ta hukumar Hisbah din na zuwa lokacin da shugaban hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya yi sakamakon yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da jami’an hukumar ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a Kano.

A ƴan kwanakin da suka gabata ne, Hisbah ta kama shahararriyar ƴar tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata baɗala a jihar Kano lamarin da hukumar ta ce ke lalata tarbiyyar matasa.

Hukumar ta kuma aika ta zuwa kotu wadda kuma ta tura ta gidan gyaran hali.

Bayan an aika ta gidan gyaran hali ne kuma aka wayi gari da labarin sakinta daga kurkuku, abin da ya yi ta tayar da ƙura a tsakanin al’ummar jihar inda wasu ke ganin da hannun gwamnati a sakin nata – zargin da gwamnatin ta musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here