A.A Rano ya baiwa fiye da magidanta ‘Dubu 200’ buhun shinkafa ɗaya da Naira Dubu 20 kowanne su

0
1215

Fitaccen attajirin nan da ke jihar Kano a arewacin Nijeriya, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano wanda aka fi sani da A. A Rano ya fara rabawa kowanne magaidanci buhun shinkafa ɗaya tare da kudi naira dubu ashirin a yankin karamar hukumar Rano.

A duk watan azumi dai Alhaji Auwalu Rano ya kan yiwa al’umma wannan rabon kayan abinci tare da ba su kudi naira dubu ashirin domin rage radadin rayuwa tare da fuskantar watan azumi cikin salama.

Al’ummar ƙaramar hukumar Rano sun bayyana jin dadinsu tare da yin godiya bisa wannan taimako da ya yi musu.

Taimakon dai ya zo a lokacin da tsadar rayuwa ke ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin wani mawuyacin hali musamman tun lokacin da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa hau-hawar farashin kayan abinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here