Naɗin Tijjani Gandu shi ne Irinsa na farko a tarihin jihar Kano – Sadiq Zazzaɓi

0
2052

Fitaccen mawakin Hausar nan, Sadik Zazzabi ya bayyana cewa naɗin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yiwa Tijjani Gandu a matsayin mataimaki na musamman akan harkokin nishaɗi da ayyukan masu fasaha a matsayin irinsa na farko a tarihin jihar.

Sadiq Zazzaɓi ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a jiya Laraba.

Madallah da wannan mukami Babban Mai taimakawa gwamnan na musamman akan harkokin mawaka da mawallafa.

Hakika hakuri, juriya da jajircewa sun taka rawar gani matuka wajen samun nasarar #TijjaniGandu
Allah ya taya ruko yasa albarka Ameen.

Babban abun sha’awa da Mai girma gwamna HE Abba kabir Yusuf ya ɗauki wannan kujera ya bawa mawaƙi, mawaƙi kuma irin Tijjani Hussaini ba shakka an saka kwarya a gurbin ta.

Ina yabawa mai girma gwamna da ya bawa mawaki wannan kujerar. Saboda abu ne wanda ba a taɓa a yi ba. A sani na tun daga 1999 zuwa yanzu babu wani gwamna a jihar Kano da ya taɓa baiwa mawaki kujera irin wannan wacce ta ke kai tsaye domin mawaka da mawallafa aka kirkire ta.

Wannan ya nuna cewa lallai mai girma gwamna ya dauki harka waka da mawaka da muhimmanci.

Tijjani Gandu dai mawaƙin siyasa ne wanda ya yi waƙar Abba gida-gida da kuma wasu waƙoƙin fina-finan Kannywood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here