Gwamnatin jihar Kano ta bayyana ƙudurinta, na baiwa ɗaurarrun da suka kammala karatu aikin koyarwa, domin bunƙasa ilimin su.
Kwamishinan ilmin jihar, Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan, lokacin bikin taya murna ga ɗalibai 48 da suka kammala karatun sakandare, a makarantar Iinmate continue education center da ke gidan gyaran hali na Kurmawa a nan Kano.
Ya ce, nan ba da dadewa ba, gwamnati za ta samar da kwamitin yiwa daurarru afuwa, wanda a ciki in dai akwai waɗanda suka cancanta za su iya samun aikin.
Daga bisani kwamishinan ya yi alkawarin bada kowacce irin gudunmawar gwamnati, domin tallafar harkar koyo da koyarwar gidan gyaran halin.
A nasa jawabin, shugaban gidajen ajiya da gyaran hali na jihar Kano, Sulaiman Muhammad Inuwa, ya ce, akwai buƙatar gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wa harkar karatun gidan gyaran halin, domin ganin an sami al’umma ta gari.
Rahoton Dala FM