Duk wanda ya bayar da shawarar a baiwa Bello Muhammad Matawallen Maradun karamin ministan tsaro, bai kalli jihar Zamfara da makomar jama’arta da idon girma da arziki. Idan za a ba shi minista ikon Bola Ahmed Tinubu ne, amma harkar tsaro ba ta da ce da shi ba a yanzu. Idan a cikin nutsuwa Abin da haka ya nuna shi ne ba za a samu bakin zaren ba a Zamfara. Ba za a daina satar mutane da garkuwa da su ba. Ba za a koma noma da kiwo ba. Babu ranar da zaman lafiya zata wanzu. Dalili rikicin yana da alaka da siyasa, ‘yan siyasa da neman biyan bukatunsu suna taka muhimmiyar rawa a ciki.
Kana rantsar da Bello Matawalle, magana ta gaskiya ka hada shi fada da babu ranar dainawa da Alhaji Lawan Dare, gwamna mai ci na Zamfara. Yaya za a dauko Badaru Muhammad tsohon gwamna a hada shi tsohon gwamna a ce su je su warware takaddamar tsaro da ta shafi gaba dayan Najeriya, alhali a jihohinsu basu tabuka komai ba? Idan aiki ake so da fahimtar juna cikin nishadi da samun nasara bai dace a hada su guri guda ba. Wannan dalilin kun yarda da shi ko akwai mai wani hanzarin?
Babban abin da ya ja hankalina a ma’aikatu da aka ayyana wadanda za su kula da su, abu ne guda biyu. Na farko dorawa Olawale Edun aikin ministan kudi, sannan aka kara masa mai kula da tattalin arziki. A fakaice an kwace aikin da tsarin mulki ya baiwa mataimakin shugaban kasa na Chairman na National Economic Council. Haka kuma wannan ya toshe duk wani katabus da ministan kasafi da tsare-tsare zai zo da shi. Wannan mukamin ministan kudi daidai yake ka kira shi da matsayin mai rabon arzikin kasa. Kowacce ma’aikata aka baka, idan Olawale Edun bai gamsu ba, ba za a sakar maka da kudin aiwatar wa ba, shi ne mutum na farko da shugaban kasa zai karbi shawarwarinsa a harkar kudi. Idan an nada ka ministan Noma KO Gona, ko ministan ilimi ko ministan gidaje ko na muhalli sai ka samu sahalewarsa sannan aikinka zai yi wu. Babu wani abin murna a ciki.
Na biyu, an rantsar da Bola Tinubu a bisa sharadin zai yi wa kasar Najeriya aiki. BA shugaban kasar Yarabawa bane, koda tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi wa fasalin yadda za a mulki kasar nan cin kaca, ba daidai bane Tinubu ya dora akan kuskure. Ashe karya da yaudara aka son yi ba gyara ba. A fahimtata da aka dauko ma’aikatu aka bayar da masu kula da su, an karkata mukamai domin a biya bukatar wani yanki. Misali Cif Dele Alake tsawon shekarun da kowa ya san shi, kawarraren dan jarida ne kuma shi ne kwamishinan labarai da strategy shekara takwas 1999-2007 a Lagos. Kafin a aika da sunansa zuwa tantancewar majalisar dattijai, shi ne kakakin fadar shugaban kasa, kwatsam kuma sai ga sunansa a matsayin ministan ma’adinai daga jihar Ekiti. Babu mukamin da ya dace da shi sama da ministan labarai. Kenan da akwai wani abu a kasa boyayye. Idan ka dauko ma’aikatar sufurin da manyan ayyuka da lantarki da sabuwar ma’aikatar Marine/Blue Economy da kasuwanci da masana’antu da kimiyya da fasaha da kirkira, so ake yi a karfafawa yankin kudu, a wofintar da arewa. Mafi dacewa shi ne a gwama ministocin Najeriya a tsakanin kudu da arewa domin su yi wa kasar aiki. An soke ma’aikatar Neja Delta, an ce NDDC ta wakliceta, amma an kirkiro sabuwa domin a karfafawa yankin South West. Wane sabon tunani aka yi domin karfafar arewa a inda suke da Comparative Advantage.
Wani abu da na lura sosai da shi, shi ne yadda aka bayar da mukamin kananan ministoci. Kura ce da shan bugu, shi kuma gardi da karbe kudi. A bisa lissafin zabe, jihohin arewa maso Yamma sune aka fi baiwa Bola Ahmed Tinubu kuri’a fiye da yankin Yarabawa. Misali, Kano ta bada kuri’a sama da dubu 500, an bata kananan ministoci biyu, wadanda basu da alaka da abin da Kanon ta shahara da su. Bil asali ma, ita Dr Mariya Bunkure, an sanya ta karkashin namiji mai fitina, halinsa maras kyau ya shahara. Kaduna bata ma da ministan, Katsina tana da ministoci biyu, Dangiwa da Musawa kwararru ne, shin zasu yi tasiri da zai mamaye Najeriya, a ji a jiki ana gwamnati?
Na san Tinubu da akariba’ihi suna da ajandarsu, kuma akanta suke tafiya, haka anan arewa ma ya kamata a samu manufa da bukatu, sai a yi aikin da duk zasu shafi Najeriya. WATAKILA kun fahimci hanzarina akan rubutun da nayi a jiya. Zamu kasa kunne don mu ji kuma mu ga yadda zata kasance. A yi hakuri dani
Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano – Najeriya.