Ɗan Majalisar Tarayya a Kano ya ƙaddamar da bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 300 a mazaɓarsa

0
457

Kimanin mutum 300 ne suka amfana da tallafin sha ka tafi wanda ɗan majilisar tarayya mai wakiltar Wudil da Garko ya ƙaddamar.

Tallafin na zuwa ne a dai dai lokacin da al’umma ke cikin kunci da matsin rayuwa tun bayan da gwamnatin tarayya ta amince da cire tallafin man fetur.

Ɗan majalisar tarayyar Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, ya ƙaddamar da tsarin na sha ka tafi da zai dinga zaƙulo mabambantan mutane daga sassan ƙananan hukumomin biyu a duk ƙarshen wata domin basu tallafin dubu biyar (₦5000) domin amfanin yau da kullum.

Shirin sha ka tafi wani tsari ne da mahaifin ɗan majalisar marigayi Alhaji Kamilu Ado Isa Ajiyan Makama ya fito dashi a lokacin da ya jagoranci ƙaramar hukumar Wudil a tsakanin shekarun 1999-2003.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da bada tallafin Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, cewa yayi ” mun zaɓi dawo da wannan tsari ne tun bayan tsawon shekaru (kamar yanda wani makaho ya bani labarin cewa; sun manta irin wannan a rayuwarsu); duba da yanayin wahalar rayuwa da ake ciki.

”A don haka muka ƙaddamar da waɗanda zasu gabatar da irin wannan tallafi su kimanin mutum 40 da suma zamuna boyansu albashi duk wata domin zaƙulo mutanen da su ka can-canta daga mazaɓunmu na ƙananan hukumomin Garko da Wudil, ta hanyar bibiyar mutanen (maza da mata) 300 har garuruwansu domin basu wannan tallafi”.

A yayin taron dai ɗan majalisar ya jagoranci aza tubalin ƙaddamar da sanya fitilu masu amfani da hasken rana wato (Solar light) a wasu sassa na ƙaramar hukumar Wudil tare da bada tallafin kayan aiki ga asibitocin dake ƙananan hukumomin Garko da Wudil domin tallafawa harkar lafiya.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗar da wakilin gwamnan jihar Kano, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso kuma mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin siyasa da wakilin Sanatan Kano ta Kudu Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila da tsohon kakin majalisar jihar Kano mai girma Alhaji Gambo Sallau da kuma Alkasim hussaini shugaban cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here