Masarautar Gombe da ke Arewa maso gabashin Najeriya ta naɗa mataimakiyar Sakare Janar na Majlisar Dinkin Duniya, Amina J Mohammed, sarautar Sarauniyar Wajen Gombe.
Mai martaba Sarkin Alhaji Abubakar Shehu Abubakar lll ne ya tabbatar da haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau juma’a
“Mai Martaba Sarkin Gombe Alh. (Dr) Abubakar Shehu Abubakar lll, CFR. Ya tabbatarwa Hajiya Dr. Amina J. Mohammed sarautar (Sarauniyar Wajen Gombe).
Hajiya Amina J Mohammad :- Tsohuwar ministan muhalli na tarayyar Najeriya kuma mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya dake New York a kasar Amurka”
Amina Mohammed ta fara shiga Majalisar Dinkin Duniya ne a shekarar 2012 a matsayin mai baiwa Ban Ki-moon tsohon babban sakataren Manofofin Ci Gaban Karni Na Majalisar Dinki Duniya (MDD) shawara Ta musamman da alhakin tsare-tsaren ci gaba.