Atiku ya buƙaci Kwankwaso da Peter Obi su haɗa hannu da shi wajen binciken Tinubu

0
421

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen Najeriya na 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci sauran ƴan takara na hamayya, Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso su haɗa ƙarfi da shi a ƙoƙarinsa na bincike kan takardun karatun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja a yau ranar Alhamis.

Ya ce abin da yake fafutuka a kai shi ne tabbatar da bin diddigi domin yin adalci da kuma gaskiya a Najeriya.

Atiku dai ya shigar da ƙara kan shugaban kasa Bola Tinubu game da takardunsa na karatu a jami’ar jihar Chicago.

Ya bukaci samun takardun ne domin su zama shaida ga zarginsa na jabun satifiket din Tinubu na CSU.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here