Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC ta janye ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yanke a gaban kotun ɗaukaka ƙara kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.
Hukumar ta INEC ta sanar da janye ƙarar ne a cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan wata 6 ga watan Oktoba, tare da sa hannun Sulaiman Alkali, Shugaban sashin shari’a na Hukumar.
“An umarceni daga hedikwatar hukumar zabe ta ƙasa domin sanar da cewa babu wani dalilin zuwa kotu domin ɗaukaka ƙara akan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi akan kujerar gwamnan Kano”
“Ɓangaren da ke lura da sashen shari’a na Hukumar INEC a matakin ƙasa da kuma babban kwamishinan hukumar mai kula da shiyyar Kano, sun yi umarni da a janye batun ɗaukaka ƙarar tare da miƙa dukkanin wani batu mai nasaba da batun ɗaukaka ƙarar zuwa ofishin hukumar zabe da ke Kano”
A ranar Laraba 20 ga watan nan na Satumba ne kotun wadda ta saurari ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar da hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bai wa Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris na 2023 ta soke nasarar.
Kotun wadda ta gabatar da hukuncinta ta manhajar Zoom ta ce tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne ya ci zaɓen.
Ta ce ta soke ƙuri’a 165,633 da ta ce aringizo ne aka yi wa ɗan takarar jam’iyyar NNPP, wanda tun farko hukumar zaɓe ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.
Tuni dai lauyoyin Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP suka yi fatali da hukuncin inda su ka garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin farko.