Kano Times

Nothing but authentic

Wallahi babu wanda na ke son in aura sai ‘Jaki’ – Murja Kunya

Fitacciyar yar Tik Tok Murja Ibrahim Kunya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta bayyana cewa babu wanda ta ke so ta aura kamar Jaki.

Murja Kunya ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok kamar yadda Kano Times ta samu kwafin bidiyo.

A cikin faifan bidiyon mai tsahon fiye da minti ɗaya da Murja Kunya din ta yi masa taken I love you Jaki, ta bayyana cewa da a irin ƙasashen Amurka ta ke ko wata ƙasa daban babu abin da zai sa ba za ta auri Jaki ba.

Ni fa ko duk duniya babu wanda na ke so kamar jaki, wallahi da a irin ƙasar Amurkawa ko wani gurin na ke da Jaki zan aura. Ina son Jaki baya son raini, bai shiga harkar kowa ba kuma babu wanda ya isa ya shiga harkarsa, sannan kuma Tsirara ya ke yawo.” In ji Murja Kunya

Idan za a iya tunawa dai Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Gida Gida ta bayyana cewa za ta yi wa jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya aure a cikin zawarawan da jihar ta yi. Sai dai kuma ba a ga fuskar Murja a cikin jerin amaren ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *