Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya zargi gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da cewa tana kokarin yin shekara takwas a kan mulki, inda ya ce hakarsu ba zai cim ma ruwa ba.
Ko da yake bai ambaci sunan Tinubu ƙarara a cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani ba, amma bayanansa sun nuna da shi yake.
Malamin ya kuma ce takarar Musulmai biyu da jam’iyyar APC ta tsayar a zaben da ya gabata ba ta da amfani kuma munafukai ne suka goyi bayanta.
Ya kuma yi zargin cewa kodayake ’yan Arewa ne suke kula da Ma’aikatar Tsaro, amma ya ce ’yan Kudu ne ke juya akalarta.
Sheik Gumi ya kuma caccaki Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, wanda ya bayyana a matsayin “aminin Shaidan” musamman kan yadda yake kokarin kulla alakar tsaro da kasar Isra’ila.
Ya ce, “Ina wadanda suka goyi bayan takarar Musulmai biyu? Munafukai marasa kishin kasa. Yanzu ga shi nan ana shirin mayar da Abuja wani bangare na Tel Aviv (babban birnin Isra’ila), ba ku ji sun yi shiru ba? Ai sun san me suke yi.
“Wani shiri ne kullalle. Wasa da hankalinmu ake son yi. So suke su yi shekara takwas, kuma Insha Allahu ba za su samu dama ba.
“Za su zo lokacin zabe su yi watsi kamar yadda ake watsa wa kaji tsaba, shi ke nan. Sai su zo suna raba wa mutane taliya, wannan babbar matsala ce a zaben da ya gabata,” in ji malamin.
Sheikh Ahmed Gumi dai dama a baya ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin manufofin jam’iyyar APC musamman a bangaren tsaro da tattalin arziki.