Manoma a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun koka akan yadda wadansu da zargin ɓarayi ne ke shiga gonakinsu su na yi musu satar kayayyakin amfanin gona da su ka shuka.
Malam Usman Surajo wani manomi da ke karamar hukumar Rano ya bayyana cewa ɓarayi sun shiga har cikin gonar Albasarsa inda su ka sace ta baki ɗaya.
Malam Usman ya ƙara da cewa “Na je Gona da nufin cire albasata kawai sai na tarar an cireta gaba ɗaya. Ban samu ko tushen albasa ɗaya ba.”
Haruna Sabo, wanda manomin shinkafa ne a yankin karamar hukumar Bunkure ya bayyana yadda ɓarayi su ka sace masa shinkafar da ya shuka.
“Na je gonata domin in duba halin da shinkafar da na shuka ta ke domin in saka ranar da zan yanketa sai na tarar an yanke fiye da rabin gonar.”
“Abin ya bani mamaki tare da jefani cikin takaici la’akari da irin yadda na kashe kuɗi da sauran ɗawainiya tsahon lokaci domin ganin na samu abin da zan rufawa kai na da iyalaina asiri“
Wasu manoma da jaridar Kano Times ta tattauna da a karamar hukumar Kibiya da Garun Malam su sun bayyana cewa a halin da ake ciki akwai manoma da yawa da su ke kwana a gonakinsu domin gadi tare da fakon ɓarayin da su ke musu satar kayan amfanin Gona.