Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 9 Sun Sace Wasu A Katsina

0
303

Ƴan bindiga sun kashe dan sanda da fararen hula takwas tare da yin garkuwa da mutane da dama a karamar hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina.

A daren Lahadi ne dandazon maharan suka kutsa garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin garin ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa har yanzu ba a iya tantance yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

Wannan harin dai na zuwa makwanni da gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da rundunar ƴan sintiri da ta yi wa laƙabi da Community Watch Corps domin magance matsalar tsaro a sassan jihar.

Sabuwar rundunar ƴan sintiri ta jihar Katsina wadda aka ƙaddamar tana da jami’ai 1,500 waɗanda za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen wanzar da tsaron, musamman a garuruwan da ake fama da harin ƴan bindiga a Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here