Kano Times

Nothing but authentic

Fiye da Mahaddata Alƙur’ani Ɗubu Ɗaya Ne Su Ka Yiwa Gidan Kwankwaso Tsinke Don A Tantancesu

Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun bayyana cewa sama da mutum 1000 Maza da Mata Mahaddata Qur’ani ne su ka halarci taron tantancewa da za a gudanar a yau litinin a gidan tsohon gwamnan jihar Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso da ke kan titin miller a unguwar Bompai.

Tun da farko mataimaki na musamman ga Sanata Rabi’u Kwankwaso kan harkokin yada labarai Saifullahi Hassan ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook a safiyar yau litinin.

Tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayyana kudurinsa na ɗaukar nauyin karatun mahaddata Alƙur’anin tun daga matakin Primary zuwa Sakandare har zuwa Jami’a.

Sanata Rabi’u Kwankwaso a wajen tantancewar

A ranar Asabar ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya buɗe MIQRA, Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani Mai Girma. An buɗe cibiyar ce a gidan tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso.

A wani shiri daga cikin shirye-shiryen taya tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso murnar cikar sa shekaru 67, Gwamna Abba Yusuf ya buɗe ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani, wadda aka raɗa wa suna Majidaɗi Institute for Qur’anic Research and Advancement (MIQRA).

An sadaukar da cibiyar ne ga mahaifin Kwankwaso, Musa Sale Kwankwaso. Kuma an gina cibiyar a gidan Kwankwaso da ke kan titin Miller Road, Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *