Hukumar NYSC reshen jihar Kaduna ta buƙaci al’umma da su ci gaba da bayar da kariya gami da taimako ga duk wasu masu hidinmtawa ƙasa da ke yankunansu.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Daraktan yaɗa labarai ta NYSC da ke Kaduna.
Ta bayyana hakanne a lokacin da ta ke isar da saƙon alhini ga iyaye da ‘yan uwa marigayiya Grace.
A cewar Miss Eddy, mai hidinmtawa ƙasar Joel Grace Chalya mai lambar KD/23A/4384 ta gamu da ajalinta ne a lokacin da suka fito motsa jiki tare da ƙawayenta.
In da daganan ne wasu ɓata gari suka yi amfani da wannan dama wajen kasheta tare da tafiya da wayar hannunta.
Ta tabbatarwa da iyayen Grace cewar a yanzu haka su na aiki da jami’yan tsaro don ganin an zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki don hukuntasu.