Wasu da har yanzu da ba a tantance ko su waye ba, sun yi garkuwa da iyayen tauraron ɗan wasan Colombia Luis Diaz wanda ya ke taka leda a kulob na Liverpool.
Kungiyar ta Liverpool ce fara sanar da faruwar lamarin, a inda ta bayyana alhininta gami da jaddada bayar da haɗin kai don ganin an samu damar kuɓutar iyayen ɗan wasan nata.
Shi ma a lokacin da yake tura saƙon alhininsu, shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Colombia Mr Gustaro ya bayyana cewar kawo yanzu an samu nasarar bayyanar mahaifiyar Diaz, mahaifinsa ne har yanzu ba a san halin da yake ciki ba.
Daga ƙarshe ya yi kira da masu ruwa da tsaki don ganin an kuɓutar da mahaifin na sa ba tare da ɓata lokaci ko wata matsala ba.