Ranar Asabar 28 ga watan Oktoban shekarar 2023, mafi yawa daga al’ummar jihar Jigawa sun wayi gari da aikin tsaftace muhallansu.
Wannan aikin-sa-kan, ya samu karɓuwa sosai ga matasa a yankuna da dama na jihar, yanda suka furfuto don kwashe magudanun ruwa, kwalbatoci, da ma share bakin titi da lunguna da saƙo na unguwanninsu.
A zagayawar da wakilin Kano Times ya yi a garin Gumel na jihar Jigawa ya yi tozali da masu aikin hidimtawa ƙasa gami da masu zaman gidan gyaran tarbiyya a cikin masu wannan aikin na tsaftar muhalli.
Wakilinmu ya lura da cewar an dakatar da zirga-zirgar motoci baki ɗaya har zuwa ƙarfe 10 na safe lokacin da aka kammala aikin a dokance.
A zantawarsa da mutane da dama akan titin zuwa Kano, da zuwa Hadejia da ma Maigatari, mutane da dama sun yaba da wannan ƙuduri da gwamnati ta bijiro da shi, domin ko ba komai tsafta na cikin abu na gaba a addinin Muslunci, kuma ta kan taimaka wajen raguwar yaɗuwar cututtukan zamani.
Idan ba za a manta ba, mai girma gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi FCA a ranar talata 22 ga watan Ogustan 2023 ya ƙaddamar da kwamatin da zai tsara, tare da fito da hanyoyin da za a tsaftace muhalli a faɗin Jihar.
Kwamatin wanda kwamishinan muhalli Dakta Nura Ibrahim Ɗan Doka ya ke shugabanta tare da sauran membobi da suka haɗa da iyayen ƙasa, da jami’yan tsaro da ƙwararru akan fanni muhalli da kuma sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu suka halarta.
Gwamnan ya tabbatar musu da tsaftar muhalli na daga cikin ƙudirorinsa guda goma sha biyu (12) da ya ke son samun nasararsu a mulkinsa.
Wannan aikin tsaftar muhalli zai ci gaba da kasancewa duk Asabar ɗin ƙarshen wata na miladiyya.