Ba mu da buƙatar ministan ƙwadago a gurin tattaunawar da zamu yi – NLC

0
206

Ƙungiyar ƙwadago mai ƙunshe da gamayyar sauran ƙungiyoyin da ke fafutukar ganin an zartar da dukkan ƙudurorin da aka zartar na tattaunawarsu da gwamnatin tarayya, sun saki sabon sharaɗi akan tattaunawar da za a yi yau Litinin.

Tattaunawar dai ta samo asali ne dalilin gayyatar da shugaban ma’aikatar fadar shugaban ƙasa ya yi, don ganin an samu daidaito da fahimtar juna akan halin da ake ciki daga ɓangaren gwamnati.

Sai dai sharaɗin da ƙungiyar ta bayar na cewar muddin Minista Lalong na ƙwadago zai halarci zaman, to tamkar gayyar za ta watse ne nan take.

Rahotannin da Kano Times ta tattaro sun bayyana cewar akwai wata jiƙaƙƙiya da ta haɗo ɓangarorin biyu akan wata matsala da ta faru da ƙungiyar NURTW.

Fatan da Femi Gbajabiamila ya ke son su cimma shine ganin batun da ƙungiyar ke yi na sake tsunduma sabon yajin aiki, an kawar da shi. Sai kuma yi wa ƙungiyar bayanan yanda aikin rabon tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai zai kasance ga ‘yan ƙasa.

Idan za a iya tunawa a farkon watan Oktoba ne ƙungiyar ta tsunduma wani yajin aiki dangane da jinkirin da ake samu na batun bayar da tallafi da kuma kawo sauƙi ga al’umma. Sai dai kwamitin da aka kafa tsananin ɓangaren gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadajon ya samar da wasu shawarwari da mafutar yanda ya kamata a tunkari lamarin ba tare da ɓata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here