Wasu Mutane Biyu Sun Mutu Yayin Wanke Tankin Man Dizil a Kano

0
170

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu, wadanda suka mutu a lokacin da suke wanke tankar man dizal, a hanyar Katsina da ke kan titin Baban Gwari, a karamar hukumar Fagge.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga sifeto Abubakar Surajo cewa wasu mutane biyu, Philip Osando mai shekaru 40 da kuma Philip Emmanuel mai shekaru 35 sun makale a cikin wata tankar man dizal.

Saminu ya ce, rahotanni sun nuna cewa, mutanen biyu, dukkansu ma’aikatan wata cibiya ce, an umurce su ne da su wanke tankin domin zuba wani man dizal din.

Jami’in hulda da jama’ar ya bayyana cewa, duk kokarin da direban tankar ya yi domin ceto su, hakan ya ci tura, wanda hakan ya sa ya yi ta kururuwadon kawo musu dauki.

Ya yi nuni da cewa, da isar su tawagar ceto ta hukumar, ta kwashe su a sume, tare da kai su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Saminu ya kara da cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta fara wani bincike, domin bankado sababin mutuwar mutanen biyu.

Ya kuma shawarci jama’a da su kasance masu takatsan tsan a koda yaushe, tare da kai rahoton faruwar lamarin da ya shafi fadawa ruwa, da rushewar gini, da hadurran titi da kuma gobara, zuwa ofishin hukumar kashe gobara mafi kusa.

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, a shekarar da ta gabata wani mai aikin janareta a Kano ya rasu a lokacin da yake kokarin kwaso man dizal daga cikin wani tanki.

KHADIJAH ALIYU

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here