Ƴan Fansho A Jigawa Za Su Ci Gajiyar Tallafin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur

0
429

A kokarin ta na ganin ta ci moriyar tallafin gwamnatin tarayya, kungiyar ‘yan fansho ta kasa reshen jihar Jigawa ta fara tattara sunayen ‘ya’yan kungiyar domin cin gajiyar shirin bada tallafin rage radadin cire tallafin man fetur na gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Umar Sani Babura ya bayyana haka a zantawar sa da manema labarai a Dutse.

Alhaji Umar Sani Babura ya bayyana cewar, uwar kungiyar ‘yan fansho ta kasa ce ta basu umarnin aike mata da cikakkun sunayen ‘yan fanshon domin amfana da shirin bada tallafin.

Yana mai cewar, a zancen ma da ake yi yanzu suna tattara muhimman bayanan ‘yan fanshon.

Ya ce bayanan da suke tattarawa kuma suka fara turawa sun hada da sunan dan fansho da karamar hukumarsa da mazaba.

Sauran sun hada da lambar asusun ajiya na banki da lambar BVN harma da katin shaidar zama dan kasa wato NIMC.

Alhaji Umar Sani Babura, ya bukaci ‘yan fanshon da basu bada bayanan su ba, dasu himmatu da turowa domin a gudu tare a kuma tsira tare.

Shugaban yayi nuni da cewar, akwai ‘yan fansho fiye da 17,000 a jihar ta Jigawa.

Yace ana sa ran ‘yan fanshon zasu amfana da tallafin naira 20,000 na tsawon watanni 3.

Umar Babura, yace tuni Kungiyar ‘Yan fansho reshen jihar ta rubuta takarda ga Gwamna Umar Namadi bisa bukatar ganin gwamnatin jihar ta shigar da ‘yan fansho cikin wadanda za su ci moriyar samun tallafin rage radadin cire tallafin man fetur.

Kazalika, ya kuma yabawa ‘ya’yan Kungiyar bisa yadda suke basu cikakken hadin kai da goyon baya a dukkanin al’amuran Kungiyar.

USMAN MOHAMMED ZARIA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here