Ƴan bindiga sun kai wa shalkwatar rundunar ƴan sanda hari a Adamawa

0
409

Wasu ƴan bindiga sun kai wa shakwatar rundunar ƴan sanda a ke Yola da sanyin safiyar Laraba, matakin da ya jefa mutanen yankin cikin rudani.

Shalkwatar ƴan sandan na tsakiyar Jimeta ne a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.

An riƙa jin ƙarar harbi da bindiga na tsawon minti 30 akalla, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar Daily Trust.

Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai ya ce an shawo kan lamarin, sannan ba a san ko su wane ne suka kai harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here