Ƴan bindiga sun hallaka shugaban jam’iyyar PDP a jihar Imo

0
331

Shugaban jam’iyyar PDP a gundumar Ife/Akpodim/Chokoneze da ke ƙaramar hukumar Ezinihitte Mbaise a jihar Imo, Smith Chiedoziem Anyanwu ya rasa ransa bayan da wasu ƴan bindiga suka harbe shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar PDP a jihar, Lancelot Obiaku ne ya shaida wa manema labarai aukuwar lamarin a Qwerri, babban birnin jihar.

Obiaku ya ce, “Lallai gaskiya ce hakan ya faru.” Sai dai bai yi ƙarin bayani ba, amma tun ranar Alhamis aka kashe mutumin.

Wasu waɗanda lamarin ya auku a gabansu sun shaida wa manema labarai cewa: “An kashe shi ne a gaban matarsa. Mutum biyu ne bisa babur suka kai masa hari, bayan sun tambayi matarsa inda yake. Daga baya da suka gan shi, sai suka harbe shi da biniga har sai da suka tabbatar ya daina numfashi.”

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda Henry Okoye bai amsa tambayoyin da ƴan jarida suka yi masa kan kisa Mista Anyanwu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here