Kano Times

Nothing but authentic

Kotu ta buƙaci Gwamnan Kano ya biya Alhassan Ado Milyan 25 kan zargin ɓata suna

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Naira miliyan 25 kan haddasa rudani da damuwa ga dan majalisar tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Hon Alhassan Ado Doguwa.

Hakazalika, kotun ta kuma soke umarnin da gwamnan ya ba Atoni-Janar na jihar na sake duba shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisa.

A zaman kotun na ranar Juma’a, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya umurci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da kada ya sake taba ƴancin dan’Adam na mai kara Alhassan Ado Doguwa ko kuma tsoma baki a abin da ya shafe shi.

Idan za a iya tunawa dai a ranar 1 ga watan Maris ne, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gurfanar da ɗan majalisa Alhassan Ado Doguwa a kotun majistre bisa zargin harbin mutum uku a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An tuhumi ɗan majalisar tare da wasu mutum 13 da hannu a kisan kai da janyo jikkatar mutane sakamakon harbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *