Daga hawan Bola Tinubu mulki an kashe ƴan Najeriya sama da dubu 5 – Beacon

0
308

An kashe ‘yan Najeriya sama da dubu 5, yayin da aka sace dubu 2 da 263 tun daga lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dare kan karagar mulki a cikin watan Mayun da ya gabata.

Kamfanin Beacon Consulting da ke nazari kan matsalar tsaro ya bayyana haka a cikin wani rahoto da ya fitar a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka zafafa hare-harensu kan al’umma musamman a jihohin arewacin Najeriya.

Rahoton ya ce, a cikin watan Yuni kadai na wannan shekarar, an kashe ‘yan Najeriya har guda 854, inda a cikin watan Yuli aka kashe 552, yayin da a cikin watan Agusta aka kashe 638.

Sai kuma wadanda aka kashe a cikin watan Satumba da adadinsu ya kai 581, sai kuma a cikin watan Oktoba da aka kashe dubu 1 da 127, yayin da aka kashe dubu 1 da 308 a cikin watan Nuwamban da ya gabata.

Kamfanin na Beacon Consulting ya zargi gwamnatocin Najeriya da gazawa wajen aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata domin ingnata sha’anin tsaro a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here