Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kananan hukumomin Gaya da Albasu da kuma Ajingi a zauren majalisar dokokin Najeriya, Dr. Ghali Mustapha ya ziyarci yan wadannan ƙananan hukumomi da su ke samun horon aikin soji a barikin sojoji na Bokavu da ke birnin Kano.
Dr. Ghali Mustapha Tijjani
Dr. Ghali Mustapha, wanda ya samu wakilcin Malam Aliyu Adamu Hungu, ya kai ziyarar ne da nufin ƙarfafawa matasan da su ke samun horon aikin soji gwiwa tare da ganin sun samu nasarar shiga aikin na soji ba tare da an samu tangarɗa ba.
Wakilin Dan Majalisar ya ce sun kawo wannan ziyarar domin ganin cewa matasan da su ka fito daga yankunan sun samu nasarar cikar burinsu kamar yadda mu ka ɗaukar musu alkawari na ganin cewa an yi duk mai yiwuwa.
“Mun zo nan domin ganin matasanmu da su ka fito daga kananan hukomomin Albasu da Gaya da kuma Ajingi sun samu nasarar matsawa zuwa mataki na gaba”
“Kuma mai girma Dan Majalisar Taraiya, Dr. Ghali Mustapha yana da wani shiri na musamman da zai inganta rayuwar matasan wannan musamman ta hanyar samar musu da ayyukan yi da jarin sana’o’i domin dogaro da kai.” In ji Aliyu Hungu