Harin Bam Kan Masu Mauludi: Tudun Biri Ya Daɗa Nuna Mana Haƙiƙarmu

0
451

Harin Bam da aka kai garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna ya haska mana irin zaman karya da munafunci da gafala da rudar kai wanda muke yi a wannan zamanin.

Wasu da suke je garin bayan harin sun yi bayanin cewa gari ne na musulmi amma katutun jahilcin da ke garin bashi misaltuwa. Kowanne nau’i na jahilci za ka iya samun sa a wannan waje, tun daga rashin sanin yanda ake tsarki da sallah da sauran aiyukan ibada, balle uwa uba sanin Allah da kadaita shi. Gari ne da yake da matukar kishirwar sanin matakin farko na ilimin addini, irin wanda a cikin birane ko yan boko aqida zaka iya samu sun san wasu. Babu makaranta ko kwaya daya ta addini babu malami.

Idan ka zo fuskacin rayuwa kuwa, halin da suke ciki abin babu kyaun gani kuma babu dadin ji. Duk wani abu na wajibin da ya kamata mutane su rayu da shi to yana matukar karanci a can. Babu makarantun boko, kai a takaice babu wani abu kwaya daya da za ka nuna na alamun gwamnati a wajen, in banda kaburburan wadanda gwamnati ta jefowa bam. Ga bakin talauci ga duhun kai.

Yan boko da suke cika ko ina da surutu game da inganta rayuwa, gabadayan hankalin su iya birane ne, babu ruwansu da irin halin matsi da talauci da kauyawa ke fama da shi. Biliyoyin kudin da ake turowa jihohi babu mai jin cewa akwai bukatar a inganta rayuwar mutanen can. Sai an samu wani abu sannan su yi amfani da wannan abin wajen nuna cewa an taba mutan su, alhali su suka fi kowa zaluntar su. Ko lokutan zabe a rura wutar kamfen da addini domin bukatar kawai ta adadin ce ba ta rayuwar masu adadin ba! Ai idan mutanen Kano, misali, basu ankara da halin da mutanen kauyukan su ke ciki ba, na Kaduna bai kamata su zama haka ba, for obvious reasons.

To haka daruruwa ko dubban kauyukan mu suke a tsahon shekaru. Idan ka dubi yanda muke fafatawa da juna a birane zaka rantse da Allah kewaye da mu babu wadanda suke bukatar mu koya musu tsarki da sallah da tauhidi. Mun kafa rassa a ko ina cikin birane amma fa kauyuka na can ciki bamu damu ko bamu ma san da su ba.

Ba ina cewa gabadaya ba a aikin bane, akwai jarumai kuma zakakuran ma’aikatan musulunci da suke kwana su tashi cikin wannan aikin. Suna barin iyalan su su shiga kauyuka suna koyar da addini kuma suna kiran wadanda ba musulmi ba. Ko sunan su ba zaka taba ji ba, saboda fagen aiki ne ba na zance ba. Kuma akwai masu hali da suke taimakawa iya gwargwadon hali ga masu wannan aikin. Amma karancin nasu ya yi yawa kwarai da gaske. Idan da damuwar da muka nuna a harin bam din nan zamu nuna rabin haka game da addinin mutanen mu na kauyuka da rayuwar su to da cikin shekara guda sai mun ga kyakkyawan canji.

A1998, muna dawowa daga Ikko, na ga jerin gwanon motocin mishan tun ina kirgawa wallahi sai da na hakura, suna dawowa su kuma daga garuruwan mu sun je yada nasu addini. A lokacin na sha mamaki. Saboda mota biyu ce da mu kacal ta fita wa’azin maguzawa da koyar da addini. Wasu bayn Allah ne masu hali suka bayar kuma suna zuwa ana fita da su. Wasu lokutan rashin kudin mai ma hana fitar yake yi. Amma naga wannan jerin gwanon na ‘yan mishan motoci daruruwa!

A lokacin, bayan mun dawo gida, bana mantawa, karshen shekara ne, na sayi jarida sai na ga labarin budget din da kungiyar suka yi na shekara mai zuwa domin da’awa ya kai biliyan guda! Mu fa a lokacin ma idan muka je wajen wasu da muke kyautata musu zato domin su shigo su taimaka ko ayi aikin da su cewa suke yi “Me ya hada ku da Maguzawa kuma!?”

Bangaren ma’abota aikin addini da na ‘yan bokon mu gabadaya ne muka gaza a wannan janibin. Kawai muna siyasar bangaranci ne da kuma siyasar duniya da mutanen da suke bukatar kulawar mu alhali mun yi watsi da su. Sai an ga Bahaushe ko Bafilatani kirista a kasashen waje a cika social media da surutun kwana biyu.

Zakakuran da suke ta aiki a kasa ba tare da mun san suna yi ba Allah ya taimake su, kuma Allah ya juyo da hankulan malaman mu da masu kudi da masu mulki zuwa ga wannan matsalar da take tamu ce zalla.

Muhammad Mahmud ya rubuto daga Kano, Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here