Kungiyar ‘yan boko ta Tijanniyya wato “International Tijjaniyya Burotherhood” ta bukaci ‘yan Izala su bar ‘ya’yan kungiyar su sakata su wala wajen yin wazifa a masallatan jami’o’i.
Kungiyar dai da ke da malamai da dalibai ‘yan Tijjaniyya a jami’o’in Najeriya, ta bayyana korafin ne a taron ta na shekara- shekara a Abuja.
Taron wanda ya samu halartar ƙungiyar dalibai ta ‘yan Tijjaniyya a jami’o;i wato TIMSAN ya nuna Tijjanawan ba su samu karfin da su ke bukata a kungiyar dalibai Musulmi na makarantun Najeriya ba da hakan ya sa a ke daukar wasu ayyukan ibada na ‘yan Tijjaniya sun wuce gona da iri.
A bayaninsa, Farfesa Muhmmad Mustapha Gwadabe na jami’ar Ahmadu Bello ya ce kalubalen ya shafi dalibai ne amma ba hukumomin jami’a ba.
Farfesa Muhammad Mustapha Gwadabe na ABU Zaria lokacin da ya halarci taron ‘yan kungiyar Tijjaniyya na shekara.
Shi ma shugaban kungiyar dalibai na TIMSAN Muhmmad Auwal daga jami’ar Ilorin ya nuna su akidar Sufanci su ke kai da Shehu Ibrahim Niasse ya jaddada.
Taron wanda ya gudana a masallacin kasa na Abuja ya samu halartar Tijjanawa maza da mata daga sassan Najeriya.
Yayin da Salafawa ko ‘yan Izala a Najeriya ke sukar Sufawa da aikata bidi’a, Sufawa na cewa a’a a bar mu su akidar su don ba kowace bidi’a ce bata ba.
VOA Hausa