Jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ba shi yake zawarcin shiga APC ba, sai dai idan jam’iyyar ce take neman ya shige ta a yadda mutane suke yaɗa zancen.
Kwankwaso, wanda ya yi takakar shugabancin Nijeriya a 2023 ya bayyana hakan ne a matsayin amsar tambayar da aka yi masa a wata hira da ya yi da ƴan jarida ranar Alhamis, kan batun komawarsa APC ko haɗewarsa da wasu jam’iyyun kasar.
A cikin hirar, Kwankwaso ya zargi abokan hamayya da cewa sun dinga tare shi daga ganin Shugaban Kasa daga 2015 zuwa 2019.
“To wannan karon ma da aka zo abin da suka tsara ke nan, cewar kada mu shiga can (Villa). Na ce haka ne? To a ci daɗi lafiya.”
Leave a Reply