Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Isma’il James, dan shekara 32, bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa a cikin kamfanin sarrafa Buhuna Fas Agro, dake rukunin masana’antu a unguwar Sharada dake jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Kiyawa ne ya sanar da hakan ga gidan ga manema labarai, da yammacin Lahadin nan.
Isma’il James wanda ake zargi da yin kisan
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce matashin James ana zarginsa ne da kashe abokin aikin nasa mazaunin unguwar Ja’en Dango dake karamar hukumar Gwale, mai suna Tukur Adamu dan shekara 32, bayan da suka samu rikici a kamfanin.
Ya kara da cewa bayan faruwar lamarin ne wasu fusatattun matasa suka yi yunkurin kona kamfanin inda jami’an tsaro su ka tarwatsa matasan tare da kama mutum 13.
Da yake ƙarin bayani kan kashe Tukur din, matashi James ya ce, rikicin ya samo asali ne biyo bayan yadda su ka samun matsala da shi a wajen aiki, amma dai yayi nadamar kashe Tukur din, inda ya ce inda ya san zai yi sanadiyyar mutuwar wani da bai zo Kano ba.