
Al’ummomin wasu garuruwa a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a yankunansu.
Mutanen yankunan ɗauke da kwalaye sun yi ta rera waƙoƙin kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki.Image caption: Mutanen yankunan ɗauke da kwalaye sun yi ta rera waƙoƙin kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki.
Mutanen yankin sun koka kan kan taɓarɓarewar tsaro, musamman yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da sace mutane, domin neman kuɗin fansa.
Wani mazaunin garin ya shaida wa sashen Hausa ma BBC cewa ‘yan bindigar sun addabe su ba dare ba dare inda suke sace mutane da dukiyoyinsu.
Mata na daga cikin mutanen da suka halarci zanga-zangar ta lumana. Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa