Ranar Hausa Ta Duniya: Bahaushe da Harshen Hausa

0
233

Daga Ibrahim Hamisu

Ba na nufin na ja ku da nisa wajen doguwar gabatarwa, don gudun gajiyarwa, ba kuma zan yi sassarfa ba, burina ku karanta a natse, duka dai domin ku fahimci wane ne Bahaushe a cikin wannan takaitacciyar maƙalar.

To wane ne Bahaushe?

Bahaushe shi ne wanda ya ke jin Hausa ya ke magana da Hausa, kuma al’adunsa da dabi’unsa duk irin na Hausawa ne.

Shi kuwa Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana Bahaushe da cewa “Wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe bane, to kai ma ba Bahaushe bane. ‘Na aro wannan ma’aunin ne bisa cewa Hausanci ƙirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali: A ƙasar Turawa, in a cikin iyaye da kakanninka akwai baƙar fata, to ko ka fi madara fari a matsayin bakar fata kake.

To amma a cikin littafin ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano (2006), an bayyana cewa “Bahaushe shi ne haifaffen mai magana da harshen Hausa da rayuwa irin ta Hausawa.”

Idan mun lura za mu samu cewa dukkanin wata ƙabila, jama’a ko al’umma to tana da nata harshen da take gudanar da harkokinta na yau da kullum da shi, misali Balarabe da harshensa na larabci, Bature da harshensa na Turanci, da kuma Bayerabe da harshensa na Yarbanci.

Harshen Hausa kuwa harshe ne da ya yi fice a yammacin Afirka, wato Nigeriya, kuma harshe ne da ya ke bunƙasa kamar wutar daji inda ya laƙume harsuna da dama wasu ma suka ɓata baki daya, wasu kuma suka zagwanye babu su ba alarmarsu.

Masana sun yi hasashen cewa sama da mutane Miliyan 150 ne suke amfani da harshen Hausa a matsayin harshen amfaninsu na yau da kullum a faɗin a duniya.

Kazalika wani bincike ya nuna cewa harshen Hausa ya na cikin yaruka mafi saurin yaɗuwa a duniya. Ko a shekarar 2020 majalisar dinkin duniya ta bayyana harshen Hausa a matsayin na 11 a cikin harsuna 70,250 da ake amfani da su a duniya. A Nigeriya kuwa da muke da harsuna 525. Kididdiga ta nuna cewa fiye da kashi 60 cikin na mutanen Nigeriya suna jin Hausa. harshen Hausa shi ne mafi dadewa tare da yin fice musamman a arewacin ƙasar.

A wannan rana ta 26-8-2023 da muke bikin ranar Hausa ta duniya; A dunƙule za mu iya cewa Hausawa wata al’umma ce da ta samo asali daga Afirka ta yamma, kuma mutane ne masu riƙo da al’adu da dabi’unsu na gargajiya, musamman wajen Abinci da Tufafi da al’amuran aure da haihuwa da abinda ya shafi sana’a da kasuwanci da neman ilimi da mu’amala a tsakanin dangi da abokai da kuma shugabanni.

Ibrahim Hamisu Dan Jarida ne kuma dalibin Hausa a Jami’ar Bayero, Kano, ya rubuto daga Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here