Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu bakwai sakamakon fargabar bazuwarsa a yankuna daban-daban, kamar yadda Ministan Ilimi na kasar Gabriel Attal ya bayyana ranar Juma’a.
“An gano kudin-cizo a makarantu da dama… Ina ganin sun kai makarantu 17, kuma a yanzu da nake magana da ku, an rufe makarantu bakwai saboda wannan matsala,” a cewar Attal a hira da gidan talbijin nan France 5.
Gwamnatin Faransa ta gudanar da taruka daban-daban a wannan makon domin gano girman matsalar yaduwar kudin-cizo a yayin take karbar bakuncin Gasar Kwallon Rugby ta Duniya sannan take shirin karbar bakuncin Gasar Olympics ta 2024.
Tun da farko, Ministan Ilimi ya aike wa da kamfanin dillancin labarai na AFP yana cewa an rufe makarantu biyar masu dalibai 1,500.
A farkon makon nan, hukumomi sun sanar da rufe makarantu biyu — daya a Marseille da daya a garin Villefranche-sur-Saone da ke wajen birnin Lyon na kudu maso gabashin Faransa — domin raba su da kudin-cizo.
“Muna da makarantu kusan 60,000 kuma wannan lamari ya shafi gomman makarantu ne kawai, amma gaskiya lamarin yana karuwa,” a cewar Attal. “Ana bukatar daukar matakan gaggawa, don haka za mu yi feshin magani bab dare babu rana.”
Ya kara da cewa sun hada gwiwa da Ma’aikatar Lafiya da hukumomin kul da kiwon lafiya na larduna kuma an “amince da wasu kamfanoni” da “shugabannin makarantu za su rika tuntuba domin daukar mataki nan-take.”
Labari mai alaka: Algeria za ta sa ido don hana kudin-cizo shiga kasarta ‘daga Faransa’
Ana sa rai za a sake bude wani dakin karatu wato laburare da ke Amiens ranar Asabar bayan an rufe shi tsawon kwanaki saboda an gano kudin-cizo a wuraren da mutane suke karatu, a cewar shugabar birnin Brigitte Foure a hira da AFP.
Ta kara da cewa karnukan da ke sansano abubuwa ba su ji duriyar kudin-cizo ba a dakin karatun bayan an yi masa feshin magani.
An yi amannar cewa ana samun kudin-cizo a akalla gida daya cikin goma a fadin Faransa a shekarun baya-bayan nan, kuma galibi yana bukatar feshin magani sau da dama wanda da ke bukatar kashe kudin da yawa kafin ya mutu.
Aan gano kudin-cizo a tashar jiragen kasa ta Paris da tashar jiragen kasa masu gudun-tsiya da kuma filin jirgin sama Charles De Gaulle.