A shekarar 2003, gwamnatin Kano, a kokarinta na bunkasa fahimtar addini cikin jama’a, ta sayi wani dan shafi a fuskar jatidar Daily Trust inda a kullum ake kawo fassarar Kur’ani. An faro tun daga Fatiha ana tafiya har aka shiga su Ali-Imran da Nisa’i.
Ai kuwa da aka zo kan ayoyin jihadi da umurnin yanda musulmi za su mu’amalanci makiyan su wadanda suka dauki makami a kan su, sai wani tsohon gwamnan soja, a Arewa, ya kasa jurewa. Ya fito ya soki gwamnatin Kano da kokarin tayar da fitina da kiran jihadi a kan wadanda ba musulmi ba, da kuma yada kiyayya tsakanin ‘yan Najeriya.
Fassara fa Kur’anin kawai ake yi da turanci, babu ko sharhi, balle a ce an shigar da wata fahimtar. Daman wannan mutumin, lokacin yana gwamna a 1980’s (ko 90’s ne?), ya taba fitowa karara yace ya ji kunyar kasantuwarsa musulmi, saboda musulmi sun kare kansu daga harin da makiyan su suka kai musu a jihar, inda aka yi asarar rayuka.
A 1994-95 (ina jin), lokacin da marigayi Sheikh Ahmad Muhammad Bamba karatun littafin Bukhari ya biyo da shi ta kan babin jihadi, saida aka yi tataburza da wasu mutane a Kano. Suka zarge shi wai da ruruta wutar fitina saboda ya karanto babin jihadi. Suka tayar masa haikan da kutunguila da sauran su. Haka dai Allah ya ba shi tabbata, kuma ya kare shi daga sahrrin su.
Wadannan ‘yan misalai ne da suke nuna maka irin yanda idan mutum bai san addini ba, ko kuma ya zabi ya yi musulunci irin wanda turawa suka yarda da shi, ba zai taba iya yarda da musuluncin Annabi Muhammadu ba. Domin su daman sun fassara musulunci a matsayin addinin tashin hankali. Shi kuma wannan ta yi masa tasiri. Gani yake duk wani abu da zai nuna tirjiya ko kwatar kai ko tabbatuwa a kan manufa ko kuma riko gam-gam da addinin to extremism ne (zafin addini).
An riga an saka shi a defensive, kariya kawai yake yi (kuma watakila har ga Allah da ikhlasi yake yi, saboda iya abinda ya sani kenan). Har sai ta kai shi zuwa ga kore abinda yake tabbatacce a addinin.
Wannan shine halin da wasu suka samu kan su a ciki. Saboda gazawar mu na wayar musu da kai da kuma yi musu bayani filla filla, har ta kai suna ganin wasu abubuwan da suke lalura ne ma a addinin kamar baki ne. Duk da ina sane da cewa akwai masu yi da gangan domin su daman layin su shine yakar duk wani abu da zai karfafi musulunci da musulmi, kamar yan boko aqida da abokan su ‘yan madakila.
Yanzu ta yaya zai zama bakon abu ga musulmi wai don an ce ya ki kfirai? Abu guda ne yake faruwa. Da zarar an ce su makiya ne sai mutum ya kalli wani makocin sa wanda ba musulmi ba kuma mai kirki da kyautatawa. Ko kuma wani dan ball din da yake so. Ko kuma wani dan fim din da ya kwanta masa a rai, da sauran su.
Baka san cewa musulunci ya kasa su aji-aji ba? Akwai masu yakar addini kai tsaye, wadanda sune mafi sharrin su, kuma dole mu yi kiyayya da wadannan, dole mu yi musu tanadi, dole mu yi musu muguwar addu’a. Akwai wadanda ba ruwan su da mu, basu yake mu ba, kuma basu fidda mu daga gidajen mu, ko kasashen mu ba. Wadannan Allah bai hana mu mu’amalar duniya da su, ko mu kyautata musu, ko mu yi musu adalci ba.
Hatta cikin makiyan akwai wadanda da makami suke yakar mu, akwai wadanda basa son mu amma su ba combatants bane, hukuncin su daban. Akwai wadanda ba ruwan su, rayuwar su kawai suke yi. Basa hana wa a musulunta kuma basa kokarin sukan musulunci, hukuncin su ba daya yake da masu kashe mu ba.
Babban abinda ya bani mamaki shine duk ayoyin Kur’ani da suke bayani kan gabar da ke tsakanin musulmi da makiyan sa. Duk tulin hadisan da suke nuna kyamar kfirci da tarbiyyantar da musulmi a kan riko da addnini da kyamar kfirci, wai sai gashi yau an wayi gari wasu baligai suna mamaki don an ce a dinga fadawa yara abinda makiyan su ke yi wa musulmi. Ciki har da wanda yace wai shi malamin islamiyya ne fa! To wai Kur’anan da suke gidajen mu ba ma karantawa ne? Ko kuma bamu san abinda ke ciki bane? Ba mu da masu fassarar Hausa ne, idan larabcin namu bashi da karfi?
Musulunci fa ba lusarin addini ba ne. Addinin zaman lafiya ne, kuma na yaki ne. addinin ilimi ne, kuma na jajircewa ne. Addinin ci gaban duniya ne kuma na tsantsar bautar Allah ne. Addinin kwalliya ne kuma na aiki-ba-kama-hannun yaro ne. Addini ne da ya kunshi shugabanci da tattalin arziki da. Addini ne da ya hade duk wani bangare na rayuwa. Ba iya masallaci kawai yake ba.
Babu abinda ya kamata mu fahimta kamar addinin mu.
Muhammad Mahmud ya rubuta daga Kano – Najeriya