Wata sanarwa da ofishin kula da ƙasashen waje ya futar ranar Asabar, ta yi kira da a tsagaita wuta a hare-haren da ake ci gaba da kai wa a Palastinu, musamman yankin zirin gaza.
Ministan harkokin ƙasashen waje Yusuf Tuggar shi ya sawa sanarwa hannu a yammacin Asabar 28 ga watan Oktoban 2023.
Tuggar ya ce kawo yanzu an yi asarar rayuka kimanin dubu tara a wannan gumurzu da ake ci gaba da yi. In da ya ƙara da cewar mafi yawan waɗanda aka hallaka ƙananan yara ne, sai mata da kuma masu rauni. Wanda hakan ya saɓawa dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa da membobin majalissar ɗinkin duniya suka rattabawa daftarin hannu jimilla.
Ofishin jakadancin ya haskaka cewar kawo yanzu matsalar da ake fuskanta ta ruwa, abinci da kuma magani a yankin na Gaza ba ƙaramar barazana ba ce. Wacce ta ke buƙatar dubuwa a gaggauce.
Wannan gumurzu dai da Isara’ila ta ke jagoranta a Gaza, ya samo sanadi ne dalilin wani harin bazata da ƙungiyar Hamas ta kai a yankin Kudancin Isara’ilan.
Yayin wancan hari, ƙungiyar ta kashe Isara’ilawa da dama, gami da ‘yan ƙasashen waje. Daganan suka yi garkuwa da wasu masu yawa a cikin yankin na zirin gaza.
Wannan mummunan rikici dai shi ne mafi muni a gumurzun da ɓangarorin biyu suka yi sau biyar a tarihi.
Tun da lokacin da ƙungiyar Hamas ta karɓi ragamar shugabancin Palastinu a shekarar 2007 ake ci gaba da samun rashin lafiya a yankin na zirin gaza da ma wasu sassa na gabas ta tsakiya.