Jihar Kano na kan gaba a masu kamuwa da cutar Mashaƙo -NCDC

0
359

Hukumar kula da kuma kandagarkin cututtuka ta ƙasa wato NCDC ta bayyana cewar a yanzu cutar Mashaƙo ta karaɗe kimanin jihohi 20 na Najeriya tare da birnin tarayya Abuja.

Bayanin hukumar ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar da cutar ke yi wa yara da ma masu manyan shekaru a faɗin ƙasar.

A cewar hukumar, a cikin jihohi 20 da suke fama da cutar, jihar Kano ce ta farko da ta ke da rahotan cutar kimanin mutane 15,060.


Daraktar Hukumar ta kuma haskaka cewar mutane 9,478 ake da tabbacin cutar ta kamasu, sauran kuma su na kan matakin gwaji.

Dr. Adetifa ta ƙara da cewar a yanzu akwai cutar a cikin ƙananan hukumomi kimanin 137 a cikin jihohi 20 na Najeriya.


Ta ce kaso 71 cikin 100 na masu fama da cutar ‘yan shekara ɗaya zuwa sha huɗu ne, sai kuma kaso ɗaya cikin ɗari wanda yara ne da ba su kai shekara guda ba.

A tattaunawar da ta yi da manema labarai a satin da ya gabata a ofishin hukumar da ke birnin tarayya, Dr. Adetifa ta ce tuni an tura kwamitocin kar-ta-kwana a yankuna da sassan da cutar ta shiga. Sai dai ƙalubalen rashin tsaro da suke fuskanta na kawo musu cikas wajen shiga wasu lunguna don yin allurar rigakafi.

Kawo dai yanzu tuni an yi wa yara kimanin miliyan biyar allurar rigakafin a faɗin ƙasar. Yayin da Kano ta ke kan gaba da rigakafin miliyan ɗaya da dubu ɗari daya da sha daya, da ɗari uku da goma.

Sauran jihohin da ke ci gaba da yi wa yara allurar rigakafin sun haɗar da Jigawa, Kaduna, Bauchi, Borno da kuma Katsina, ya yin da dubunnan yara suka je don yi musu allurar rigakafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here