
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa matatar man fetur da ke jihar Kaduna za ta fara aiki a ƙarshen shekarar 2024.
Matatar man fetur din na ɗaya daga cikin matatun mai huɗu a Najeriya da su ka daina aiki.
Idan ba a manta ba an bayar da kwangilar gyarar matatun man a shekarar 2021, kan dala biliyan 1.5.
Haka kuma a cikin watan Faburairu, kamfanin mai na NNPCL ya ba da kwangilar gyarar matatar ga kamfanin Daewoo.
Ƙaramin ministan mai na Kasa Heineken Lokpobiri, ya ce yayin da aiki ya yi nisa yanzu ana sa ran za a kammala gyaran matatar, zuwa ƙarshen shekarar 2024.
Lokpobori, ya yi wannan bayanin ne a lokaci da ya kai ziyarar gani da ido gurin ayyukan da ake yi a matatar man fetur din da ke Kaduna a ranar Asabar.
Shima babban manajan NNPCL, Mele Kyari, ya ce lallai za a mika wa gwamnatin Najeriya matatar man a karshen 2024, kuma a wannan lokaci za ta fara aiki tuburan.