
Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Kasar Ebira, Ohinoyi Abdul Rahman Ado Ibrahim (CON) rasuwa.
Mai Martaba Abdul Rahman Ado Ibrahim, ya rasu ne a fadarsa da ke garin Okene a Jihar Kogi kafin wayewar garin Lahadi.
Ya koma ga Mahaliccinsa ne yana da shekaru 94 a duniya, kuma bayan shekaru 25 a karagar mulkin Masarautar Kasar Ebira da ke Jihar Kogi.
Ya hau mulki ne a shekarar 1997 bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori.