Fitaccen mawakin nan na Hausa, Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka ya yi kira ga al’ummar jihar Kano musamman magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya da su fito ƙwansu da ƙwarta domin halartar zanga-zangar lumana da za su gudanar a yau Asabar.
Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana haka ne a shafinsa na TikTok kamar yadda Kano Times ta gani.
“Kowa ya yi sallama da gidansa da iyalansa da ƴaƴansa a fita kar a dawo sai da ƴanchi a dawo da Rai da ƴanchi ko kuma a dawo ba rai amma da ƴanchi“
A makon jiya ne dai zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kwanan nan kan zaben gwamnan jihar.
Kalaman na Naziru Sarkin Waƙa na zuwa ne dai a lokacin da magoya bayan jam’iyyar NNPP su ka kira zanga-zangar lumana a yau Asabar da misalin karfe uku na yamma.
Matakin na zuwa ne bayan bayyanar kwafi na hukuncin Kotun Daukaka Kara, wanda ake zargin ya saɓa wa hukuncin baki da ta sanar a makon da ya gabata, inda ta jaddada hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na kwace nasarar Abba Kabir Yusuf na NNPP, ta bai wa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC.