Ƴan Sanda Sun Cafke Hadimin Gwamnan Kano Bisa Zargin Karkatar da Tallafin Kayan Abinci

0
517

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a ofishin sakataren gwamnati Tasiu Al’amin-Roba da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin karkatar da kayan abinci na rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnati ta bayar don rabawa al’umma kyauta.

An kama wadanda ake zargin ne a wani gidan ajiyar kaya da ke Sharada dauke da buhuhunan shinkafa da masara sama da 200.

Da yake tabbatar da cafke mutanen kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Hussaini Gumel, ya ce sun gano cewa wadanda ake zargin suna sauyawa kayan abincin buhu da nufin siyar dasu ga al’umma, sabanin yadda gwamnati tace a raba kyauta.

Hussaini Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike na gaskiya.

A jiya asabar gwannan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gidan a ajiyar kayan, bayan an gano cewa karkatar da kayan abincin don siyarwa, inda gwamnan yayi alkawarin yin bincike tare da hukunta masu hannu a cikin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here