Murnata ɗaya, Buhari da ransa yana gani, an yi abin da gwamnatinsa ta sa aka lalata karatun jami’a da shi. Amma wataƙila cirewar ba wani cikakken amfani za ta yi ba, domin aikin gama dai ya riga ya gama. Yawancin jami’o’inmu a yanzu suna cikin tsananin wahala. Tsarin IPPIS ɗin nan, da a ce an shirya adalci a cikinsa, ta hanyar cikashe wawaka-wawakan giɓukan da ya zo da su, da ƙila ba shi da wata matsala, amma suna kallo mutanen jami’a suka ce zai cutar da mu, amma suka yi ƙememe, wai su ga masu mulki. Ko ina mulkin yake yanzu? Oho!
A lokacin Buhari, na yi wani rubutu a kan wasu mutum 6 zuwa 7 da suka lalata ilimin jami’a a Najeriya. Su ne suka dage a kan IPPIS ɗin nan, saboda wata manufarsu ta ɓarnatar da kuɗin ƙasa, wadda daga baya ta fara fitowa. Kawai bayan na yi rubutun, sai na ƙi sakar shi, saboda yadda a lokacin wasu suka dinga zage-zage saboda rashin fahimta. Amma yanzu ga wasu daga cikinsu, da wasu masu goya musu baya, rukuni biyu. Ga su kamar haka, daga ƙaraminsu zuwa babbansu.
6) TSOHON Akanta janar na wancan lokaci: Na manta sunansa, kuma ba ma sai na tuno ba, don ba shi da wani amfani, amma dai shi ne aka kama da zargin ya saci wasu kuɗin Najeriya da za su iya gyara matsalar ilimin jami’a gabaɗayanta. Wato ko ba komai, in ka je daf da gidan sarkin Kano, za ka ga wani gini da aka ce an ƙwace (kuma an ce nasa ne) wannan zai nuna alama na irin ɓarnar da mutanen nan suke yi. Kuma wataƙila wannan ginin guda ɗaya ne a cikin da yawa. Wataƙila wasu suna Abuja da Kaduna, ƙila ma har da ƙasashen waje. Amma shi wannan ya ma yi ƙoƙari fa, tun da gida ya dawo da kuɗin. Kuma yana yi wa al’ummar lungunsu kirki. Gaskiya yana yi musu mutunci sosai, amma dai a lokacin rigimar ASUU da gwamnatin Buhari, yana daga cikin na gaba-gaba wajen gaba da ASUU.
5) Ngige: Shi kuma wannan mutumin a lokacin shi ne ministan ƙwadago TSOHO. Wato mutum ne kalar ‘yan duniya sosai, wanda yake da alamun rainin wayo da ƙin jinin talakan Najeriya. In ka ji yadda ya dinga zagin malaman jami’a da gwaɓa musu baƙaƙen maganganu a lokacin, za su ba ka tausayi. Ya yi rashin albarka buhu-buhu, amma yanzu ga shi ya zama tarihi.
4) Adamu Adamu: Shi ne TSOHON ministan ilimi. Mutum ne haziƙi da ya dinga goyon bayan ASUU, har ma ya taɓa cewa ‘yan Najeriya ya kamata su zo gabaɗayansu su godewa ASUU gami da mara mata baya. Yana daga cikin waɗanda suka fi ba wa kowa mamaki a harkar. Yana samun mulki gabaɗaya tunaninsa ya juya daga masoyin al’umma zuwa abokin faɗan ASUU. Shi ma yanzu ya gama, kuma na san dai duk da Abuja za ta yi musu sauƙin zama, amma dai ba kamar a lokacin suna mulki ba. Yanzu ogan nasa ma ya koma garinsu. Ka ga ma shi sai ya dawo mu cigaba da salati da istigifari tare, kafin kuma mu ga ya Tinubu zai yi da ƙasar. Don ma dai rayuwarmu ba a hannunsu take ba, dukkansu.
3) Osinbajo: Shi kuma TSOHON mataimakin shugaban ƙasa ne, kuma tsohon Malamin jami’a kuma farfesa. An yi tunanin zai yi amfani da ƙarfin ofishinsa wajen kawo sulhu, to amma tun da yawancinsu sun mallaki nasu jami’o’in, kuma ‘ya’yansu ba a nan suke karatu ba, shi ma ya bi yarima ya sha kiɗa.
2) Buhari: Babban Oga kenan. Shi wannan ba sai na ce komai a kansa ba! Sai dai a yi shiru. Nakan tuna yadda ya dinga sakace haƙoransa a lokacin mulkinsa. Shi ma yanzu ya zama TSOHON shugaban ƙasa. Sai dai mu yi addu’ar Allah ya yafe mana zunubanmu, da mu da shi da su.
1) Talakawan Najeriya; mu muka fi kowa laifi, musamman mu ‘yan Arewa. Na ga wani rubutun Farfesa Kperogi yana cewa munafurci ne ya sa yanzu ‘yan Arewa suke cewa za su yi magana. Gaskiya kusan haka ne ni ma ba ga shi na ce muku na yi rubutu amma na ƙi saka shi ba a wancan lokacin. Duk da haka, ya kamata a gane cewa kullum ƙara ƙurzuwa ake yi, kuma kullum wasu suna ƙara wayewa jama’a. Bahaushe kuma yana cewa; “duka yau duka gobe, shi ke sa baƙin Ba’auzini tawaye!” Kuma in Buhari ya yi ba daidai ba an kauda kai, ba shi yake nuna kowa ma zai yi ba daidai ba a jure. Amma dai talakawan Najeriya sun cutar da kansu a lokacin Buhari. Duk masifar da ta taho, haka aka dinga barinta tana wucewa, don ni lokacin ma in na kalli lamarin sai in rasa mai zan ce. Abu ɗaya dai na fara ganowa a yanzu, lallai gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari abu biyu, abubuwan kuwa su ne; wayo da mugunta. Muguntar mai wayo kuwa ba ƙaramar illa ne da ita ba.
Ina dai fatan Allah ya sa Baba Tinubu ya yi mana adalci.
Ga su kamar haka don kar ku manta da su. Waɗanda suka kassara ilimin jami’o’in gwamnati a Najeriya a tunanina; amma in ba su ba ne, to waye?
6) Akanta janar na wancan lokaci
5) Ngige
4) Adamu Adamu
3) Osinbajo
2) Buhari
1) Talakawan Najeriya
©muhammadunfagge