Bola Tinubu ya sha alwashin wadata ƴan Najeriya da wadataccen abinci da lantarki a 2024

0
263

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin wadata ‘yan Nijeriya da isasshen abinci a shekarar 2024.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi na sabuwar shekara inda ya yi bita kan wasu daga cikin nasarori da kalubale da kasar ta samu tun bayan da ya karbi mulki da kuma jaddada wasu alkawuran.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatin kasar za ta noma kadada 500,000 a bana domin yakar yunwa a kasar.

“Domin samar da isashen abinci da kuma abinci mai araha, za mu kara himma wajen noma kadada 500,000 na gonaki a fadin kasar nan domin noman masara, shinkafa, alkama, gero da sauran kayan amfanin gona.

“Mun kaddamar da noman rani da kadada 120,000 a Jihar Jigawa a Nuwambar bara a karkashin Shirin Noman Alkama,” kamar yadda shugaban kasar ya tabbatar.

Baya ga noma, Shugaba Tinubu ya yi wa ma’aikatan masana’antu alkawarin aiwatar musu da sabon tsarin albashi domin dakile radadin da ‘yan kasar ke ciki.

Za mu yi aiki tukuru don ganin kowane dan Najeriya ya amfana da tsarin gwamnati. Ba za a yi watsi da burin da talakawa da masu tsananin bukata da ma’aikata ke da shi ba na samun ingantacciyar rayuwa ba.

Sakamakon haka ne ya sa za mu aiwatar da sabon tsarin albashi ga masu aiki a masana’antunmu a wannan sabuwar shekara,” in ji shi.

Haka kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa a bana za ta yi iyakar kokarinta domin ganin ta magance matsalar wutar lantarki da kuma ci gaba da gudanar da wasu ayyukan samar da wutar lantarki.

Haka kuma shugaban ya ce gwamnatinsa na ci gaba da yin iyakar kokarinta domin ganin cewa matatun mai na Fatakwal da kuma Dangote sun fara tace mai a wannan sabuwar shekara.

Tun a farkon jawabin Shugaba Tinubu, ya kara karfafa wa ‘yan kasar gwiwa dangane da wahalhalun da suke ciki tare da jaddada cewa komai zai warware nan ba da jimawa.

Shugaban kuma ya kara jaddada cewa duk wani mataki da ya dauka tun bayan karbar mulki, ya dauka ne domin ci-gaban Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here