
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi Allah-wadai da yadda ake yin garkuwa da yara da kuma sayar da ƙananan yara, waɗanda galibinsu ƙananan yara ƴan arewaci ne zuwa kudancin ƙasar nan.
Sarkin ya bayyana damuwarsa ne a jiya a Kano yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ɗan Malikin Kano, Jakada Ahmad Umar wanda ya wakilci sarkin mai daraja ta ɗaya, ya ce masarautar ba za ta ƙara amincewa da sace-sacen yara da fataucin su a jihar ba.
Ya ce lamarin ya fita daga hannunsu saboda haka dole ne a dauki matakin da ya dace domin daƙile lamarin.
“Dole ne a daina wannan mummunan al’amarin. Dole ne mu tashi mu yaƙe shi. Ba za mu ƙara la’akari da halin da ake ciki na ake sace ƴaƴanmu, ana sayar da su kuma ana canza ƙabilarsu da addininsu ba.”
“Dole ne a daina bin wannan haramtacciyar hanya. Dole ne mu tashi mu duba halin da ake ciki, abin ya wuce kima. Hakan ya fara aukuwa ne shekaru kaɗan da suka gabata kuma ya sake faruwa. Allah ne kaɗai ya san adadin yaranmu da aka sace aka sayar da su,” inji shi.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano a ranar 27 ga watan Disamba, 2023 ta ce ta tarwatsa wata ƙungiyar masu safarar mutane da ta ƙware wajen sata da sayar da ƙananan yara.
Rundunar ta ƙara da cewa an kama mutane 9 da ake zargi da hannu a ƙungiyar da ke aiki a kewayen jihohin Kano, Bauchi, Legas, Delta, Anambra da Imo.
Haka kuma ta kuɓutar da ƙananan yara bakwai waɗanda akasarinsu ƴan asalin jihar Bauchi ne.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban al’ummar Igbo na Kano, Boniface Igbekwe, ya yi tir da wannan aika-aika tare da yin kira ga hukumomi da su gurfanar da dukkan waɗanda suka kama na aikata laifin.
Wanda ya samu wakilcin firaministan al’ummar Igbo, Cif Nwaimo Efanyi, ya ce al’ummar Igbo sun samu labarin yaran da ƴan sanda suka yi garkuwa da su cikin kaduwa da damuwa matuƙa.
Ya ce ɗaukacin al’ummar Igbo mazauna Kano sun ware kansu daga waɗanda ake zargi da duk wani mummunan aiki da aka aikata da sunan su, yana mai jaddada cewa a kullum suna da burin ganin an zauna lafiya da juna.